“Na kai, yallabai. Sati biyu da suka gabata.”
“Sati biyu da suka gabata!”
Mayakin ya kyalkyale da dariya, hakama mutanen da suke bayansu.
“A cikin wannan yanayin, makiyan mu zasu tabattu a kan bari daga sun ganka.”
Thor yaji shi yana konuwa da rasin ji dakai. Dole yayi wani abu. Ba zai bari yakare haka ba. Mayakin ya juya don ya tafi – amma Thor ba zai iya barin hakan ya faru ba.
Thor yayi taku zuwa gaba sai yayi ihu: “Yallabai! Kana son kayi kuskure!”
Sanda kowa a taruwan jama’a ya ja numfashin tsoro, yayinda mayakin yasake sayawa ya juyo a hankali.
Yanzu sai ya matsa goshinsa a cikin fushi.
“Wawan yaro,” mahaifinsa yace, ya cafke Thor a kafada, “koma ciki!”
“Bazanje ba!” Thor yayi ihu, ya girgiza ya kubuta daga cafkewan mahaifinsa.
Mayakin yatako zuwa gaba ya nufi Thor, sai mahaifinsa yaja dabaya.
“Kasan horon da ake yiwa wanda ya zagi dan Silver?” mayakin ya tambaya da barazana.
Zuciyan Thor nata daka, amma ya san bazai ja da baya a yanzu ba.
“Dan Allah ka yafe masa, yallabai,” mahaifinsa yace. “Shi karamin yaro ne kuma----”
“Ba dakai nake Magana ba,” mayakin yace. Da wani kallon raini, ya tilasta wa mahaifin Thor ya juya ya koma.
Mayakin ya juyo zuwaga Thor.
“Bani ansa!” yace.
Thor ya hadiye yawu, ya gagara Magana. Ba haka yaga kasancewan lamarin a kwakwalwansa ba.
“Zagin dan Silver na daidai da zagin sarki da kansa ne,” Thor yace da ladabi, yana mayar da abin da ya koya daga tunani.
“Haka,” inji mayakin. “Wannan na nufin zan iya maka bulala arba’in in naga dama.”
“Bana nufin in zageka, yallabai,” Thor yace. Inason a dauke nine kawai. Kayi hakuri. Nayita mafarkin wannan duk tsawon rayuwana. Kayi hakuri. Ka barni na samu shiga.
Mayakin ya kalleshi, sai a hankali, yanayinsa ya yiwo laushi. Bayan dan lokaci mai tsawo, sai ya girgiza kai.
“Kai karami ne, yaro. Kana da zuciyan maza. Amma ba a shirye kake ba. Ka dawo ka samemu in an yayeka.”
Da waanan, sai ya juya ya ruga, bama kallon shauran yara mazan. Ya hau dokinsa a gagauce.
Thor, rai a bace, ya kalli tayarwan tawagan; Kaman yadda suka iso da sauri, suka tafi.
Abu na karshe da Thor yagani shine yan’uwansa, azaune a bayan rumfan amalanken karshe, suna kallonsa, da rashin aminci, suna masa dariya. Ana tafiya dasu a gaban idonsa, nesa daganan, zuwaga rayuwa mafi inganci.
Daga cikin zuciyarsa, Thor yaji Kaman yamutu.
Da hayaniyan da ya kewaya shi ya kare a hankali, duk mutanen kauyen su sun kokkoma gidajensu.
“Kasan irin wawancinda kanuna, wawan yaro?’ mahaifinsa ya haura, ya kuma cafke kafadunsa. “Kasan da zaka iya bata wa yan’uwanka sa’ansu da zarafinsu?”
Thor ya ture hannayen mahaifinsa daga jikinsa da haushi, sai mahaifin ya miko hanu ya mari fuskansa da bayan hanu.
Thor ya ji zafin abin ya mayar da hararo ga mahaifinsa. Wani bangarensa, a karo na farko, yaso ya rama marin da mahaifin ya masa. Amma ya kama kansa.
“Je ka dawo da garken tumakina. Yanzu! Kuma in ka dawo, karka sa ran zan ciyar da kai. Za ka rasa abincin daren yau, sai kayi tunani a kan abinda ka aikata.”
“Watakila bazan ma dawo ba gaba daya!” Thor na ihu yana juyawa don ya tafi, ya bar gida, ya nufi su tudun bayan gari.
“Thor!” mahaifinsa ya kira da karfi. Yan kalilan din kauyawan da suka rage a kan hanya sun saya suna kallo.
Thor ya fara shi ba gudu ba shi kuma ba tafiya ba, sai ya fara gudu, yanason ya nisanci wannan gurin gwargwadon abinda ya samu. Baima san shi ya fara kuka ba, hawaye sun mamaye fuskarsa, yayin da duk mafarkun da ya taba rike wa a zuciyarsa suka cikaro da mummunan mutuwa.
SURA NA BIYU
Thor yayita yawo a cikin daji na sa’oi, cike da fushi, kafin daga karshe ya zabi wata yar tudu ya zauna, hannayensa a nade a kan kafafuwansa, yana kallon sararin Allah. Ya kalli bacewan amalankun, yayita kallon kuranda suka tayar na wasu sa’oi bayan su sun bace.
Bazasu sake kawo wata ziyara ba. Yanzu ya kamu da kaddaran zaman kauyen nan na shekaru kenan, yana jiran wata zarafin – idon ma sun dawo kenan. In kuma mahaifinsa ma ya yarda kenan. Yanzu zai zama shi da mahaifinsa, su kadai a gida, kuma tabattace mahaifinsa zai huce haushinsa a kanshi. Zai cigaba da kasancewa bawan mahafinsa, shekaru zasu yita tafiya, sai shima ya karasa rayuwansa Kaman nashi, a makale da dan karamin rayuwa, na leburanci – alhali yan’uwansa sunsamu yabo da sanuwa. Jininsa nata tafasa da rashin ji dakai a kan lamarin duka. Ba wannan rayuwan yakeso ba. Kuma shi ya san da haka.
Thor yacigaba da wasa kwakwalwa ko akwai abinda shi zai iya yi, ko ta wani hanya domin ya juya lamarin. Amma babu komai. Kaman haka kaddara da rayuwa ya rubuta masa zai kasance.
Bayan zaman sa’oi, ya tashi ba karfin gwiwa, ya fara komawa saman sananen tudun, Karin hawa akan Karin hawa. Bamusu, ya koma zuwaga garken, zuwa ga tudu mai tsayin. Yayinda yake haurawa, rana ta fadi a sama kuma na biyun ta kai kololuwa, ta sa yanayi mai rowan ganye a kan wuri. Thor ya dauki lokacinsa, a yayinda ya dinga tafiyan a hankali, ya ciro majajjabarsa daga kugunsa, fatan marikan a kode saboda shekarun datayi ana amfani da ita. Ya shiga cikin buhun da shima ke kugunsa ya tabo zabbabun duwasunshi, kowanne yafi mabiye dashi taushi, zabbabu daga mafi kyawun koramu. Wani lokacin yakan harbi tsunsaye; a wassu lokutan kuma, beraye. Wannan hali ne da ya sabar ma kansa a cikin shekaru. Da farko, baya samun abinda ya harba; saikuma, a lokaci daya, ya harbi abu mai tafiya. Tun daga lokacin saitinsa ya tabbata. Yanzu, wurga duwatsu ya zama masa jiki – kuma ya taimaka masa wurin huce haushi. Yan’uwansa suna iya sara itace da takwafinsu – amma bazasu iya harbin tsuntsun da ke tafiye da dutse ba.
Thor yasa dutse a majajjabar Kaman ba komaiba, ya dan kwanta baya, sai ya harba da dukan karfinsa, da tunanin Kaman yana wurgin mahaifinsa ne. Wurgin yasamu wani reshe a kan wata bishiya da nisa, ya kuma sauke shi farat daya. Tunde ya gano cewa shi yana iya kashe dabbabobi da suke tafiya, ya daina aunasu, yana tsoron baiwansa kuma bayason yaji ma komai ciwo; yanzun reshen bishiyoyi ne abun aunawansa. Saidai, in har, dila ya biyo garkensa. A cikin lokaci, suma sun koyi kiyayewa, sai tumakin Thor a sabili dahaka, su kafi nakowa sira a kauyen.
Thor yayi tunanin yan’uwansa, yayi tunanin inda suke a yanzu, sai ya fara taffasa. Bayan tafiyan wuni zasu isa haraban sarki. Yana ganin hoton hakan a zuciyarsa. Yana ganin isowansu ga babban buki, mutane a kayayyaki mafi kyau, suna gaishesu. Jarumai suna gaishesu. Yan Silver. Za a shigardasu, a basu wurin zama a barikin rundunan, wurin koyo a filin sarki da mafi kyawun makamai. Kowanne za a lakaba masa sunan wani sananen bafaje. Wata rana kuma, suma zasu zama fadawa, a basu dawakai, tambarin kare kasa da nasu mallakaken fili. Zasu kasance cikinsu bikibiki na kowane shekara suna kuma ci suna sha tare da sarki. Wannan rayuwa mai dadi ne. Kuma duk wannan ya zame masa.
Thor ya fara ji Kaman bayi da lafiya, sai ya nemi ture dukkan wannan tunanin daga zuciyarsa. Amma ya gagara. Wani bangaren jikinshi, bangare mai zurfi, dayake masa ihu. Yana ce masa kar ya fidda sammani, cewa yana da babban kaddara daya fi wannan. Baisan me kaddarar ba, amma yasan ba a nan take ba. Yana jin shi daban ne. Watakila ma na musamman. Kuma duk sun raina masa isa.
Thor ya kai dan tudu mafi sayi sai ha hango garkensa. Masu ladabi, haryanzu a tare, suna more kowane ciyayi suka samu da gamsuwa. Ya kirgasu, yana duba jan alamu dashi yayi a kan bayan kowanne. Jikin shi ya mutu daga gamawa. Tumaki daya ya bata.
Ya sake kirgasu, ya kuma sakewa. Ya gagara yarda: guda daya ya kauce.
Thor bai taba batar da tumaki ba, kuma mahaifinsa bazai taba