Duk da haka, Thor yayi mafi kyawun amfani da dammar da yasamu, yana samo hanyoyin da siturorinsa za su yi daidai dashi, yana daura dogayen riguna da igiya akewaye da kugun sa, saikuma, yanzu rani ta iso, yakan yanka hanayen rigunan domin hanayensa da suka riga suka yi baki su sha iska. Rigarsa da yi daidai da mattatiyar wandon alawaryonsa – kayan mallakarsa guda biyu kacal – da takalmansa da a ka yi daga mafi talautuwan patar leda, sun kai ga har kwabrinsa. Ba a yi su da patar da tayi kokusa da wadda a kayi na yayunsa dashi ba, amma ya san yanda yake sasu amfanar shi. Ya kasance tamkar alamar makiyayin dabbobi ne.
Amma fa yana da wuya a ganshi a yanayin kowa. Thor na da sayi kuma tsiriri, da marikar yarda da kai, habban masu kirki, sayyayun kumatu da idanu masu launin toka, yana kama da jarumin da baya bata. Mikekiyar gashin kansa mai launin kasa sun zubo baya a jejjere a kansa, kasa kadan da kunnuwansa, sannan a bayan gashin, idannunsa na kyalli Kaman kifin tarfasa a cikin haske.
Za a bar yan’uwan Thor suyi bacci a wannan safiyar, a basu lafiyayen abinci, kuma a tura su zuwa wurin zaben mayaka da mafi kyawun makamai da kuma sa albarkan mahaifinsa – alhali ba a ma barin shi shima ya kasance. Ya taba kokarin tayar da maganan da mahaifinsa sau daya. Sakamakon hakan bai yi kyau ba. Mahainfinsa ya kasaita hirar a hanya na kawai, kuma bai sake gwada wa ba. Lamarin ya kasance ba adalci ne kawai.
Thor na da muradin kin kaddarar da babansa ya shirya masa. Daga ganin alamun farko na rundunar gidan sarauta, zai koma gida a guje, ya fuskanci mahaifinsa, kuma, koyaki koyaso, ya bayyanar da kansa wa mutanen sarki. Shima ma zaiyi takaran shiga rundunan mayaka da shauran. Mahaifinsa bai isa ya hana shi ba. Ya ji wani kulewa a cikin sa a yayin tunanin hakan.
Ranar farkon ya dan kara haurawa, sai a lokacin da na biyun, da launin koren minti, ya fara haurowa, yana kara wa sararin samaniya wani irin haske mai launin malmo, Thor ya hango su.
Ya mike a tsaye, gashi a mimmike, yana mamaki. A nan, daga can nesa, wani mafi karancin yanayin amalanken doki, tayun sa suna tada kura zuwa sama. Bugun zuciyarsa ta karu a yayin daya ga bullowar wata kuma; sai kuma wata. Daga nan ma yana ganin amalanku masu launin gwal suna kyalli a cikin rana, Kaman kifi mai bayan zinari dayaka tsalle ya koma ruwa.
A lokacin daya kirga har goma sha biyu a cikin su, ya gagara hakuri ya kara jira. Da duukan zuciya a cikin kirjinsa, da manta garken tumakinsa a karo na farko a rayuwarsa, Thor ya juya sai ya gungura kasan tudun da tsauri, da muradin yin koma mai zata bukata domin bayanar da kansa.
*
Thor yaki ya saurara ya daidaita numfashinsa a yayin da yake gangarawa tudun a gunje, ta sakiyan bishiyoyi, rasan suna ta kwarzanan sa amma bai damu ba. Ya kai wani shararriyar fili sai yaga kauyensa: gari mai kaman yana barci a shake da gidaje masu bene daya, fararen gidajen laka masu jinkar ciyawa. Iyalen da suke cikin ta basu fi dozin kadan ba. Hayaki na tashi daga dakunan dafuwa dayake yawanci an tashi ana shirya kalacen safe. Guri ne gwanin ban sha’awa, da nisa daidai – tafiyan wuni a kan doki – daga padar sarki ga mai rabewa a kan hanyan wucewa. Wani kauyen manoma ne kawai a bakin zoben, wani karamin kusa a babban tayan masarautar yammaci.
Thor ya karasa shauran karshen hanyan a guje, ya shiga sakiyar kauyen, yana tada kura a yayin tafiyan. Kaji da karnuka sai kauce masa a kan hanya suke yi a guje, sai wata tsohuwa, a tsugune a kofar gidanta a gaban tukunya dauka da ruwanda yake taffasa, tayi masa tsaaki.
“Jeka a hankali mana Yaro!” Ta fada da karfi a yayin daya wuce a guje, ya sa mata kura a wutan cikin murhunta.
Amma kuma Thor ya wuci jin kira – ba ma ita ba, ba ma kowa ba. Ya sha kwana zuwa wata anguwar gefe, saikuma wata, yana murduwa yana juyuwa cikin hanyoyin da ya riga ya lakanta a zuciya, har ya kai gida.
Gidan karami ne, mazauni mara wani muhimmancin tsari Kaman shauran, da fararen bangon laka da jinkan zana daya hadu da bangon. Kaman yawanci, daki daya da gidan ya kunsa a rabe yake, mahaifinsa na kwana a bangare daya, yan’uwansa kuma a daya bangaren; inda gidan ya sha bambam da yawanci shine, yana da ‘yar karamar dakin dafuwa a baya, anan ne kuma a ka ware Thor ya dinga kwana. Da farko, yakan cunkusu da yan’uwansa; amma a cikin lokaci sun kara girma da rashin imani da kuma waraiyya, kuma sun mayarda rashin bashi wuri abin alfa’ari. Thor yakan ji haushi, amma yanzu yana more sararin kansa, yafi son ya nisance su. Wannan ya tabattar masa da abinda dama ya sani na cewa shine wararren gidan.
Thor ya nufi kofar shiga gidansu sai ya ruga ciki ba tsayawa.
“Baba!” ya tsala da ihu, yana numfashi da kyar. “Yan silver! Suna zuwa!”
Mahaifinsa da dukan yan’uwansa uku suna zaune a sunkuye akan shimfidar cin kalacen safe, sun riga suna sanye da kayayyakin su mafi kyawu. Da jin kalmominsa sun daka tsalle suka wuce shi zuwa waje a guje, sunata buge masa kafada a yayin wucewa aguje daga cikin dakin zuwa kan hanya.
Thor ma ya bisu waje, sai duk suka fara kallon alqibla suna saye.
“Bana ganin kowa,” Drake, babbansu, yace cikin murya mai zurfi. Da mafi fadin kafadu, gashi a yanke Kaman na yan’uwansa, idanu masu launin kasa, da siraren mara soyuwar labba, ya harari Thor Kaman yadda a ka saba.
“Haka nan nima,” inji Dross, mabiyin Drake da shekara daya kawai, mai kuma bin bayansa kullun.
“Suna zuwa!” Thor ya mayar masu. “Na rantse!”
Mahaifinsa ya juyo zuwa gareshi ya kuma riko kafadunsa da rashin tausayi.
“Kuma da yaya ka sani?” ya nemi yaji.
“Na gansu.”
“Tayaya? Daga ina?”
Thor ya dan saurara; mahaifinsa ya gano shi. Dama ya san wuri daya kawai da Thor zai iya hango su dagashi kuma shine dan kololon tudun nan. Yanzu kuma Thor ya rasa yaya shi zai mayar.
“Na…hau dan tudun –”
“Da garken tumakin? Ka san bai kamata su yi wannan nisan kiwon ba.”
“Amma yau ya kasance dabam. Ya zama mun dole na na gani.”
Mahaifinsa ya kale shi a kasa, kallon kiyyayya.
“Maza ka shiga ka dibo takwuban yan’uwanka ka haskaka zabiran su, domin su zama mafi kyawun kallo kafin mutanen sarkin su iso.”
Mahaifinsa, bayan yagama magana dashi, ya juya zuwa ga yan’uwansa, wayanda duk suke tsaye a hanya suna kallon hanya.
“Kana ganin zasu zabe mu?” inji Durs, Dan autan cikin su ukun, amma yayan Thor da shekaru uku masu kyawu.
“Zasu zama wawaye idon suka ki,” mahaifinsa yace. “Suna da karancin mayaka a wannan shekaran. Yakasance musu siririyar girbi – da basu damu da zuwa ba. Kudai ku tsaya a mike, dukkanku uku, ku daga haban ku sama ku kuma tura kirjin ku gaba. Kada ku kalli idanunsu kai tsaye, amma kar ku kuma kau da idanunku gaba daya. Kuyi karfin hali da yarda da kai. Kada ku nuna gazawa. Idon kuna son ku kasance a cikin rundunar sarki, dole kuyi kamman kun riga kun shige ta.
“Ai, Baba,” yaran sa maza uku suka ansa a lokaci daya, tare da fadawa muhalli.
Yajuyo ya harari Thor daga baya.
“Me kake yi a nan har yanzu?” ya tambaya. “Ka shiga daga ciki!”
Thor ya tsaya a wurin, yana zuciya bibiyu. Baya son yaki bin umurnin mahaifinsa, amma dole ne ya tattauna dashi. Zuciyarsa na ta daka a yayin da yake musabaka. Ya nadi ra’ayin bin umurnin zai fi alheri, ya kawo takwuban, sanan ya fuskanci mahaifinsa. Kin bin umurnin gaba gadi ba zai taimaka ba.
Thor ya ruga cikin gidan a guje, ya fita ta baya zuwa runfar makamai. Ya samu takwuban yan’uwansa uku, dukkansu abubuwa na gwanin sha’awa, da rawanin wurin rikewa na azurfa mafi kyawu, muhimman kyauta da mahaifinsa yayi bautan shekaru kafin suka samu. Ya daffo duka uku, yana mamakin nauyinsu Kaman yadda ya saba, sai ya koma ya ruga a guje ta cikin gidan dasu.
Ya gagauta zuwa ga yayunsa, ya mika wa kowa takwabi daya, sanan ya juya zuwa ga mahaifinsa.